6,728
IB Exclusive Media
🎥 IB Exclusive TV : Talk shows, interviews & cultural stories from Northern Nigeria.
🎯 Services: Videography, event coverage, decor & more.
📩 DM to book or collaborate!
📞07060840000,09042610643
📩 IBexclusive01@gmail.com
🌍www.ibxclusive.com
HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL![]()
Cikin daren dan, 'yan ta'addan Lakurawa suka kai hari cikin Masallaci a garin Dadinkowa karamar hukumar mulki ta Maiyama a jihar Kebbi![]()
A lokacin harin sun ķàşħ£ Masallata mutun 4 a cikin Masallaci dakin Allah, sannna sun raunata wasu ![]()
Yaa Allah Arewa, ana bin mu har Masallaci ana kash£wa, Allah Ka kawo mana dauki ba don halayen mu ba🙏😭![]()
✍️ Datti Assalafi
Shirin Neman Aljanna a chikin watan Ramadan kashi na (8)tare da Malama Juwairiya Usman sulaiman.![]()
Ramadan Kareem. Part 2
Lokacin da ƴan sanda za su riƙa aikata abin da suka ga dama ya zo ƙarshe - Sabon Sufeta Janar ![]()
Mukaddashin Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Mista Olatunji Disu, ya bayyana cewa zamanin yin abin da aka ga dama a cikin Rundunar ‘Yan Sanda ya zo karshe.![]()
Da yake zantawa da manema labarai na Fadar Shugaban Kasa bayan rantsar da shi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi, Disu ya ce nadin ya zo masa a lokacin da bai yi tsammani ba.![]()
Ya ce yadda Shugaban Kasar ya rika ambaton ayyukan da ya gudanar, wuraren da ya taba aiki da nasarorin da ya samu a matsayinsa na jami’in dan sanda, ya matukar taba zuciyarsa.
TIRKASHU: Baya ta haihu: APC ta sauya tsarin rabon shugabancin jam'iyya a Kano zuwa 50–50 maimakon 60-40![]()
Uwar jam’iyyar APC ta ƙasa ta sauya tsarin rabon iko a jihar Kano daga kaso 60–40 da ta amince da shi a farko zuwa 50–50 tsakanin bangaren Gwamna Abba Kabir Yusuf da bangaren tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje tare da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin.![]()
Sauyin ya biyo bayan taron karɓar Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, zuwa APC a ranar 16 ga Fabrairu, wanda ya gudana a Kano ![]()
Jaridai Daily Nigerian ta rawaito cewa taron ya bar baya da Kura, inda jam'iyyar ta lura cewa, shugabannin APC na asali ne suka tara jama'a a taron ba wai Gwamnan Kano ba, hakan ne yasa ta ce da sake, wai an bai wa mai kaza kai, in da ta sake ragewa gwamna Abba kaso 10 a cikin sittin din shi, ta kara wa bangaren Ganduje da Barau.![]()
Sabon tsarin ya tanadi rabon 50–50 tsakanin bangarorin biyu, a wani yunƙuri na tabbatar da daidaito da kuma rage rikicin cikin gida. Rahotanni sun ce shugabannin jam’iyyar a matakin ƙasa sun nuna rashin gamsuwa da yadda taron sauyin sheƙar bai jawo dimbin magoya bayan Kwankwasiyya ba kamar yadda ake zato.![]()
Duk da sauyin sheƙar wasu ‘yan majalisa, kwamishinoni da shugabannin ƙananan hukumomi 44, ana ganin tushen magoya bayan Kwankwasiyya na nan daram tare da jagoranta, Rabiu Musa Kwankwaso.![]()
A wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Kano, an cimma daidaito inda aka bai wa gwamnan kujeru 14 cikin 27 na shugabannin ƙananan hukumomi, yayin da bangaren Ganduje ya samu 13.![]()
Majiyoyi sun tabbatar wa da jaridar cewa matakin ya samu amincewar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, domin tabbatar da daidaito da ƙarfafa haɗin kai a cikin jam’iyyar a Kano.![]()
Masu sa ido na ganin sabon tsarin na 50–50 na iya rage zazzafan rikicin cikin gida, sai dai ana jiran a gani ko zaman lafiyar bangarorin biyu zai dore ko kuma sabbin rikice-rikice za su ɓulla a nan gaba.
Rahotanni na nuni da cewa wani gwamnan PDP da ’yan majalisa na shirin komawa APC
Mbappé ba zai buga wa Real Madrid wasan kofin zakarun Turai da za ta fafata da Benfica ba.
FACES OF IB-EXCLUSIVE TELEVISION![]()
At IB-EXCLUSIVE TELEVISION, we don’t just report the news; we capture the pulse of the moment. ![]()
Part of leading that charge are three of our most dynamic producers: Aisha Sadik Abubakar, Ibrahim Abubakar, and Ruqayyah Ibrahim Shehu.![]()
Their journey began in the intimate world of podcasting, where they mastered the art of the deep dive and the power of the human voice. Today, they have traded the studio mic for the high-stakes lens of television journalism. As they transition into "on-the-mark" reporters, their growth reflects our own mission: to stay ahead, stay bold, and stay exclusive.![]()
Driven by an unrelenting zeal to leave their mark on the industry, this trio is ready to transform your visions into a vivid, broadcast reality.![]()
* Instgram
* Facebook
* YouTube
@IBExclusive![]()
Join us on a journey of lights, lens and life!![]()
The future of IB-EXCLUSIVE TELEVISION isn't just coming - it’s already here!![]()
Stay Exclusive!
Wasu Rahotanni Sun Nuna Cewa, Ɗan Bello Zai Tsaya Takarar Shugaban Kasa A Nijeriya
Wata majiya mai tushe ta shaida mana hakan, ta kara da cewa shirye-shiryen tsayawar Dan Bello takarar shugaban kasa, ya yi nisa, inda kuma ake zargin wani salo ne na raba kuri'un Arewa.
Mene ne ra'ayinku
Rikici Ya Ɓarke Tsakanin Hausawa Da Inyamirai A Kofar Ruwa Ta Kano![]()
An samu faɗa tsakanin Hausawa da Inyamirai a kasuwar Kofar Ruwa da ke Kano. Fadan ya barke ne biyo bayan wani rashin jituwa inda wani Bahaushe mai tebir ya sanya ƙaramin rufin saman teburi, wanda wasu Inyamirai suka cire saboda kusancinsa da layin kasuwa.![]()
Hakan ya jawo tashin hankali, inda aka fara tayar da rikici. Sai dai, jami’an ‘yan sanda sun iso wurin da wuri don dakile ɓarkewar fadan, kafin a sami babbar matsala. ![]()
Hausawan sun yi ikirarin cewa da ba a dakile su ba, lamarin zai kara tsananta.![]()
Allah ya kiyaye gaba.![]()
Daga Hamza Abdullahi
DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnan jihar Gombe Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya ya gwangwaje fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da kyautar danƙareran sabon gida a birnin Gombe wanda zai dinga rayuwa tare da iyalansa idan ya je jihar domin tafsirin azumin da yake gabatarwa a kowace shekara.![]()
Wane irin fata za ku yi masa?
