4,868
IB Exclusive Media
🎥 IB Exclusive: Talk shows, interviews & cultural stories from Northern Nigeria.
🎯 Services: Videography, photography, event coverage, décor & more.
đź“© DM to book or collaborate!
📞 07060840000
đź“© IBexclusive01@gmail.com
🌍www.ibxclusive.com
An buƙaci duk mai son Sarautar Gung Zaar ya rubuta wa Gwamna.![]()
Gwamnatin Jihar Bauchi ta buƙaci duk ɗan ƙaramar hukumar Tafawa Balewa da Bogoro da yake son Sarautar Gung Zar ya rubuta wa Gwamna takardar buƙatar hakan ta hannun ƙaramar hukumar sa.![]()
Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwar da Daraktan harkokin Masarautu a Ma'aikatar ƙananan hukumomi da Masarautu ta Jihar Bauchi Muhammed Ali Manti ya fitar, a madadin Kwamishinan Ma'aikatar, inda ya ce an samar da Jami'ai da zasu karbi takardun a dukkan Shalkwatar ƙanana hukumomin.![]()
Sanarwar ta ƙara da cewa za a rufe karɓar takardar neman Sarautar a ranar Lahadin nan 26 ga watan Oktoba, 2025 da misalin ƙarfe sha biyu na rana.![]()
Takardar ta ƙara da cewa tuni dai an sanar da Shugabannin ƙananan Hukumomi da abin ya shafa.
Idan malami ya hau kan mimbari a na daukar shi da Camara yana aika sako film ne.![]()
A cewar Tijjani faraga Dan wasan Hausa.
Shirye-shiryen Nadin Mai martaba sarkin Gamawa HRH. Alh. Adamu Abdulkadir Dahuwa
Cigaba da sauraran isowar jami'an Gwamnatin Jahar Bauchi domin nadin mai martaba sarkin Gamawa HRH. Alh. Adamu Abdulkadir Dahuwa.
